Kungiyar Tarayyar Afirka Ta Jaddada Aniyarta Ta Cimma Muradun Karni A 2020
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i13852-kungiyar_tarayyar_afirka_ta_jaddada_aniyarta_ta_cimma_muradun_karni_a_2020
Shugaban kwamitin sulhu da tsaro na kungiyar tarayyar Afirka Isma'il Cheragwa ya jaddada aniyar kungiyar wajen cimma muradun karni a shekara ta 2020.
(last modified 2018-08-22T06:59:14+00:00 )
Nov 14, 2016 04:39 UTC
  • Kungiyar Tarayyar Afirka Ta Jaddada Aniyarta Ta Cimma Muradun Karni A 2020

Shugaban kwamitin sulhu da tsaro na kungiyar tarayyar Afirka Isma'il Cheragwa ya jaddada aniyar kungiyar wajen cimma muradun karni a shekara ta 2020.

Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa ya bayar da rahoton cewa, shugaban kwamitin tsaron na kungiyar tarayyar Afirka ya bayyana cewa akwai manyan kalu bale da suke a gaban kungiyar tarayyar Afirka a fuskoki da daban-daban, muhimmai daga ciki su ne batutuwan tsaro da tattalin arziki.

Ya ce bisa ga tsarin da kungiyar take da shi, ya zuwa shekara ta 2020 za a samu babban sauyi a nahiyar a wadannan bangarori, haka nan kuma ya yaba wa kasar Zambia kan daukar bakuncin babban taro na Afirka da ta yi a cikin makon da ya gabata.