AU Ta Kalubalanci EU Akan Albashin Sojojin Burundi Dake Somaliya
Kungiyar tarayya Afrika ta bukaci kungiyar tarayya Turai data sake nazari akan matakinta na biyan sojojin kasar Burundi dake cikin tawagar wanzar da zamen lafiya ta AMISOM a Somaliya albashi kai tsaye ba tare da ya biyo ba ta hannun mahukunta Bujumbura ba.
Wata sanarwa da kungitar ta AU ta fitar a ranar Juma'a data gabata a yayin wani taron kwamitin kungiyar mai kula da harkokin soji a birnin Adis Abeba ta ce tana adawa da wannan sabon matakin na EU na canza tsarin biyan albashi ga dakarun na Burundi dake Somaliya.
Kungiyar ta EU dai ta dau wannan matakin ne saboda kada mahukuntan Burundi sunyi amfani da kudin domin biyan wasu bukatunsu.
Saidai wata majiyar diflomatsiyar turai, kungiyar ta EU ta ce zata iya canza tsarin da zarar kungiyar ta AU ta samu wata hanya ta biyan sojojin ba tare da kudin sun bi ta hannun mahukuntan Burundi ba.
A martanin data mayar kan wannan batun gwamnatin ta Burundi ta ce wannan ma yana daga cikin matakin kungiyar ta EU na neman wargaza kasar ta Nurundi, wanda ya ce zai iya kaiwa har ma kasar ta janye dakarunta daga kasar ta Somiliya.
Kasar Burundi dai ita ce kasa ta biyu mafi yawan dakaru a cikin tawagar ta AMISOM dake yaki da kungiyar Al'Shabab data kunshi dakaru sama da 22,000.