Guinea Bissau : Ana Dakon Naddin Sabon Fira-minista
Al'umma a kasar Guinea Bissau, na ci gaba da dakon sunon sabaon fira ministan da za'a nada bayan da shugaban kasar Jose Mario Vaz ya rushe gwamnatin firaminista Baciro Dja.
A Jiya Litinin ne Mista Vaz, ya sanar a cikin wani jawabi zuwa ga 'yan kasarsa, da rushe gwamnatin firaminista Baciro Dja, da nada wani sabon firaministan da zai samu amincewar kowa cikin sauri.
Ba'a dai bayyana takaimaiman lokacin da za'a nada sabon firaministan ba, aman wata majiya a kusa da fadar shugaban kasar ta ce za'a yi nadin nan bada dadewa ba.
Wannan sabon faraminista, a cewar shugaban kasar, za a daura masa nauyin kafa wata gwamnatin hadaka, kamar yadda yarjejeniyar Conakry ta tanada, domin fitar da Guinea-Bissau daga ricikin siyasa da zaman zullumi na fiye da shekara guda.
A cikin jawabin nasa, shugaba Vaz ya bayyana cewa, ya dauki wadannan matakai bayan da ya tuntubi jam'iyyun siyasa da kwamitin kasa, wato wata hukumar tuntubar juna dake hade da fadarsa.
Sanarwar rushe gwamnatin Baciro Dja na zuwa bayan wata ziyara da wata tawagar masu shiga tsakani da shugabar kasar Laberia Ellen Johnson Sirleaf ke jagoranta ta kai a kasar domin yin matsin lamba wa masu ruwa da tsaki kan rikicin kasar akan su gaggauta aiwatar da yerjejeniyar kawo karshen rikicin siyasa da suka cimma a ranar 14 ga watan Oktoba a Birnin Conakry karkashin jagorancin shugaba Alpha Conde.