Zanga-Zangar Nuna Rashin Amincewa Da Keta Alfarmar Kur'ani A Morocco
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i13996-zanga_zangar_nuna_rashin_amincewa_da_keta_alfarmar_kur'ani_a_morocco
Al'ummar yankin Lisasafah da ke cikin gundumar kazablanka a kasar Morocco sun gudanar da wani gangami a yau domin nuna rashin amincewa da keta alfarmar kur'ani mai tsarki da aka yi a yankin.
(last modified 2018-08-22T06:59:15+00:00 )
Nov 16, 2016 15:27 UTC
  • Zanga-Zangar Nuna Rashin Amincewa Da Keta Alfarmar Kur'ani A Morocco

Al'ummar yankin Lisasafah da ke cikin gundumar kazablanka a kasar Morocco sun gudanar da wani gangami a yau domin nuna rashin amincewa da keta alfarmar kur'ani mai tsarki da aka yi a yankin.

Shafin yada labarai na Nur Press ya habarta cewa, an samu wasu kwafi-kwafin alkur'ani mai tsarki a yagea  cikin masallaci Alkhuzami da ke yankin Lisasafah a cikin gundumar Kazablanka a kasar Morocco, lamarin da ya harzuka al'ummar yankin baki daya.

Rahoton ya ce jama'a sun taru suna yin kira ga hukumomin kasar ta Morocco da su dauki matakan gagagwa wajen gano tare da hukunta duk wanda aka samu da laifin keta alfarmar kur'ani mai tsarki a wanann masallaci, wanda shi ne karo na biyar da hakan ta faru a cikin wannan wata a cikin yankin.

Limamin masallacin Alkhuzami ya ce bayan kammala sallar Isha'in jiya, wata mata ta zo ta tambaye bangaren da mata ke salla cikin masallacin, kuma bayan ta fita ne aka samu kur'anai da dama an keta su a cikin masallacin a bangaren mata.