Gwamnatin Nigeria Ta Bukaci Saudia Ta Bada Rahoton Karshen Kan Faji'ar Mina
Shugaba Muhammadu Buhari na Nigeria ya bukaci gwamnatin kasar saidia ta kammala magana dangane da mutuwar mahajjatan Nigeria 274 a Mina a lokacin Hajjin shekarar da ta gabata.
Shugaba Muhammadu Buhari na Nigeria ya bukaci gwamnatin kasar saidia ta kammala magana dangane da mutuwar mahajjatan Nigeria 274 a Mina a lokacin Hajjin shekarar da ta gabata.
Babban mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ne ya bayyana haka a jiya Asabar ya kuma kara da cewa shugaban ya bukaci gwamnatin kasar Saudia ta kammala maganar biyan diyar yan Nigeria guda 6 da suka rasa rayukansu a faduwar karfen Cren a kusa da dakin kaaba a shekarar da ta gabata sannan da gwajin DNA na yan Nigeria 35 da suka bace bayan faji'ar ta mina.
Malam Shehu Garba ya kara da cewa shugaban ya tattauna batutuwa 17 da jami'an gwamnatin kasar Saudia, daga ciki ya bukaci ta kara yawan yan Nigeria da zasu rika zuwa aiki hajja da umra a ko wace shekara. Kasar Nigeria dai tana da kujeru dubu 76 na zuwa hajji a ko wace shekara.
Karamin ministan harkokin waje Mrs Fatima Abba Ibrahim da kuma shugaban hukumar Hajji ta Nigeria Abdullahi Muhammad ne suka jagoranci zaman da jami'an Nigeria suka yi da tokororinsu na kasar Saudia.