Nijeriya: An bayar Da Belin Mai Shari'a Ngwuta
Wata babbar kotu a birnin Abuja na Najeriya ta bayar da belin mai shari'a Sylvester Ngwuta bayan da ya musanta aikata laifuka da suka hada da halatta kudaden haram da cin hanci.
An bayar da belin Sylvester Ngwuta a kan kudi naira miliyan 100 da kuma kimar da yake da ita, saidai an ce za' a ci gaba da sauraron karar a ranakun 7, 8 da kuma 9 ga watan Disamba mai zuwa.
Mai shari'a Ngwuta, wanda wani alkalin kotun kolin kasar ne da jami'an tsaron farin kaya na DSS suka cafke a watan Oktoba daya gabata, bayan sumame a gidajensu ya bayyana gaban kotun ta Abuja a yau Litinin.
An dai zargi Ngwuta da hallata kudaden haramun da yawan su ya kai sama da miliyan daya da dari shida na Euro.
Shi dai Ngwuta ya musunta dukkan zarge zarge da ake yi masa.
Yaki da cin hanci da rashawa na daga cikin alkawulan da shugaban kasar Muhammadu Buhari yasa a gaba, saidai tuni matakin ya fara shan suka da cewa bita da kullin siyasa ne kawai akeyiwa makusantan tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan.