An kashe Mutane da dama a Sudan ta Kudu
Akalla Mutane 25 ne suka rasa rayukansu sanadiyar wasu jerin hare-hare da 'yan tawaye suka kai a kasar Sudan ta Kudu
Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa ya nakalto Philip Town Lake daya daga cikin magabatan 'yan Majalisar jiha na yankin gabashin Sudan ta kudu a jiya Alkhamis na cewa kimanin mutane 25 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu 17 na daban suka jikkata sanadiyar wasu jerin hare-hare da wata kungiyar 'yan tawaye wacce ta balle daga cikin kungiyar madugun 'yan tawaye kasar kuma tsohon shugaban kasa Riek Machar ta kai a cikin 'yan kwanakin nan.har ila yau hare-haren ya raba mutane sama da dubu 20 da mahalinsu.
Dan Majalisar jiha na Jongulai dake gabashin kasar Sudan ta kudun ya kara da cewa rashin tsaro ya sanya Al'ummar yankin komawa cikin daji domin gudanar da rauywar su a can.
A watan yulin da ya gabata ne wani sabon rikici ya sake barkewa tsakanin Sojoji dake goyon bayan Shugaban kasar Salva keir da kuma masu goyon bayan tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar, lamari da ya sake jefa kasar cikin wani sabon tashin hankali, sannan kuma ya sanya fargaba na sake komawar kasar cikin yakin basasa.
MDD ta sanar da cewa rikicin Sudan ta kudu ya yi sanadiyar raba mutane miliyan daya da dubu 600 da mahalinsu wadanda yanzu haka ke sansanin 'yan gudun hijra na Majalisar dake cikin kasar, sannan wasu dubu 900 sun gudu zuwa kasashen dake makwabtaka da kasar