Sojojin Nijeriya Sun Jaddada Aniyarsu Na Kawo Karshen Barazanar Boko Haram
Babban hafsan hafsoshin sojojin Nijeriya Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai ya jaddada aniyar rundunar sojan kasar na fada da kungiyar ta'addancin nan ta Boko Haram domin kawo karshen barazanar da take ci gaba da yi ga tsaro da zaman lafiyan al'ummar kasar.
Rahotanni daga Nijeriyan sun jiyo Janar Burutai yana bayyana hakan ne a yayin da yake magana dangane da irin shirin da sojojin kasar suke da shi na kawo karshen barazanar 'yan Boko Haram din wadanda a cikin 'yan kwanakin baya-bayan nan suka dan kara kaimi da wasu hare-hare a wasu yankuna na jihar Borno inda ya ce a halin yanzu dakarun sojin Nijeriyan za su kara kai mi wajen kai hare-hare kan tungar 'yan Boko Haram din musamman wadanda suke yankunan arewa maso gabashin Nijeriyan.
Babban hafsan hafsoshin sojan Nijeriyan ya kara da cewa ya zuwa yanzu dai sojojin sun karya lagon 'yan Boko Haram din abin da ya sanya su komawa ga kai hare-hare ga yankunan fararen hula, don haka ya kirayi al'umma da su yi taka tsantsan.
Duk da irin nasarorin da sojojin Nijeriyan suka samu a kan 'yan Boko Haram din bayan hawar sabuwar gwamnatin kasar karagar mulki, amma cikin 'yan kwanakin nan 'yan ta'addan sun dawo da kai wasu hare-hare lamarin da ya sake sanya damuwa cikin zukatan mutane.