Shugaban Kasar Ivory Coast Ya Yi Garanbawul A Majalisar Ministocin Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i14407-shugaban_kasar_ivory_coast_ya_yi_garanbawul_a_majalisar_ministocin_kasar
Shugaban kasar Ivory Coast Alassane Ouattara ya gudanar da wani garanbawul a majalisar ministocin kasar.
(last modified 2018-08-22T06:59:18+00:00 )
Nov 26, 2016 03:23 UTC
  • Shugaban Kasar Ivory Coast Ya Yi Garanbawul A Majalisar Ministocin Kasar

Shugaban kasar Ivory Coast Alassane Ouattara ya gudanar da wani garanbawul a majalisar ministocin kasar.

Fadar shugaban kasar Ivory Coast e ta sanar da hakan a yammacin jiya, daga cikin muhimman canje-canjen da aka yi kuwa har da na dama safke ministan harkokin wajen kasar, tare da nada shugaban ofishin shugaban kasa Marshel Amun Tano a matsayin sabon ministan harkokin wajen kasar.

Wannan mataki dai ya zo ne sakamakon rashin cimma matsaya tare da wasu daga cikin jam'iyyun da suka shiga kawance tare da jam'iyya mai mulki domin tunkarar zaben 'yan majalisar dokokin kasar a watan gobe, inda wasu daga cikin jam'iyyun suka sanar da ficewa daga kawancen su tare da jam'iyyar shugaba Ouattara.