A Yau Ne Ake Zaben Gwamna A Jihar Ondo Na Tarayyar Nigeria
A yau Asabar ne masu zabe a jihar Ondo na tarayyar Nigeria zasu zabi wanda zai cike kujerar gwamnan a jihar cikin yan takara 28 daga jam'iyyu daban daban da suke takaran kujerar a jihar.
Hukumar zaben kasar INEC ta bayyana cewa mutanen da suka mallaka katin zabe na din din din 1,659,186 amma har yanzun 378,606 basu karbi katunan zaben nasu ba.
Daga cikin yan takara 28 masu neman wannan kujerar akwai Mr Eyitayo Jegede of the PDP, Chief Rotimi AkeredAPC, sannan a bangaren tsaro kuma an tanadar da jami'an yansanda 26'000 da jirgen Helkocta 3 yansanda na musamman rundunoni 12 da kuma yansanda na cikin ruwa masi kwalekwalen 20. Sannan shugaban yansanda Mr Ibrahim Idris ya ce a ko wace rumfan zabe zasu ajite dansan biyar.