Somaliya: Harin Kungiyar al-shaba a gabacin kasar Somaliya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i14437-somaliya_harin_kungiyar_al_shaba_a_gabacin_kasar_somaliya
Al-shabab kai hari a yankin Modag
(last modified 2018-08-22T06:59:18+00:00 )
Nov 26, 2016 15:24 UTC
  • Somaliya: Harin Kungiyar al-shaba a gabacin kasar Somaliya

Al-shabab kai hari a yankin Modag

Kungiyar al-Shabab ta 'yan ta'adda ta kai hari ne da safiyar yau asabar akan cibiyar sojojin kasar da ke yankin Modaq da ya yi sanadin kashe mutane bakwai da jikkata wasu da dama.

Bugu da kari, kungiyar ta kai wani hari a kan cibiyar 'yan sanda da ke garin Afjuyi mai nisan kilo mita 30 daga babban birnin kasar Magadishu.

Baya ga sojojin gwamnati da su ke fada da kungiyar al-shabab da akwai dubban sojojin tarayyar Afirka na tabbatar da zaman lafiya da su ke tallafa musu.

Tun a cikin 2012 ne dai kungiyar ta al-shabab wacce reshe ne na kungiyar alqaida, ta kai munanan hare-hare acikin kasar Somaliya da kuma Kenya.