Kimanin Mutane miliyan biyu ne ke bukatar taimakon gaggawa a Nijer
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa kimanin Mutane milyan biyu ne ke bukatar taimakon abinci a jumhoriyar Nijer
Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa na kasar China ya nakalto Ofishin Hukumar ayyukan agajin gaggauwa ta Majalisar Dinkin Duniya OCHA na birnin Yamai fadar milkin jumhoriyar Nijer na cewa har yanzu kasar Nijer na fuskantar matsaloli kimanin biyar wadanda suka hada da karamcin abinci, rashin abinci mai gina jiki, cututuka masu yaduwa, ambaliyar ruwan sama gami da rashin tsaro a wasu yankunan kasar.
Ofishin ya kara da cewa Ma'aikatar kiyon lafiyar kasar na fuskantar matsalar magani musaman ma na cututukar masu yaduwa kamar amai da gudawa gami mananjite, kuma a halin da ake ciki a kwai Mutane sama da miliyan biyu dake bukatar agajin gaggauwa a cikin kasar.
Duk da irin Dunbun arzikin da kasar ke da shi, kama daga kiyon dabbobi, karfar uranuin, zinari, kawayi gami Man fetur, amma har yanzu Al'ummar kasar na fuskantar matsalar tattalin arziki, inda a cikin ko wasu shekaru 10 sai kasar ta fuskancin matsalar karamcin abinci a kasar