Mutanen Kasar Sudan Sun Fara Yakin Aiki Kan Kara Farashin Makamashi
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i14515-mutanen_kasar_sudan_sun_fara_yakin_aiki_kan_kara_farashin_makamashi
Kasuwanni da mutocin haya masu zaman kansu da wasu bangarori daban daban na yan kasuwa a kasar Sudan sun fara yajin aiki na kwanaiki ukku don nuna rashin amincewarsu da karin kudin makamashi wanda gwamnatin kasar tayi.
(last modified 2018-08-22T06:59:18+00:00 )
Nov 28, 2016 07:17 UTC
  • Mutanen Kasar Sudan Sun Fara Yakin Aiki Kan Kara Farashin Makamashi

Kasuwanni da mutocin haya masu zaman kansu da wasu bangarori daban daban na yan kasuwa a kasar Sudan sun fara yajin aiki na kwanaiki ukku don nuna rashin amincewarsu da karin kudin makamashi wanda gwamnatin kasar tayi.

Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ta bayyana cewa motocin haya, kasuwanni gidajen cinabinci da sauransu duk sun dakatar da aiki a safiyar yau litinin don nuna rashin amincewar mutanen kasar kan karin farashin man fetur da kuma gas wanda gwamnatin shugaban Umar Hassan al-bashir ya sanar a cikin yan kwanakin da suka gabata.

Karin farashin makamashin ya rage tallafin da gwamnatin take yi ya kara farashinsu da 30% kuma tuna hakan ya shafi farashin kayakin abinci, magunguna da kuma sauran bukatun yau da kullum a kasuwannin kasar.

Duk da cewa makarantun gwamnati a bude suke amma iyayen sun gwamnace ajiye yaransu a gida don gudun abinda zai kai ya koma a lokacin yajin aiki na kwanaki ukku.