An Sace Wasu Jami'an Majalisar Dinkin Duniya A Kasar Sudan
Wasu mutane masu dauke da makamai sun sace wasu jami'an majalisar dinkin uku masu kula da ayyukan tallafawa 'yan gudun hijira a yankin Darfur.
Majiyoyin tawagar majalisar dinkin duniya a kasar Sudan sun bayyana cewa mutanen sun kai samame ne a kan jami'an majalisar dinkin duniya a yankin na Darfur, kuma sun yi awon gaba da jami'ai uku zuwa wani wurin da ba a sani ba.
Babu wata kungiya dai da ta dauki alhakin kai harin, kuma mahukuntan kasar ta Sudan ba su ce uffan ba kan wannan lamari, amma dai jami'an kiyaye sulhu da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya da tarayyar Afirka sun shiga gudanar da bincike kan lamarin.
Tun a cikin shekara ta 2003 ce dai aka fara rikici a yankin Darfur tsakanin kabilun bakaken fata da kuma larabawa 'yan janjawid masu dauke da makamai da gwamnatin Albashir ke mara wa baya, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane masu tarin yawa.