An hallaka Mayakan Ashabab da dama a Somaliya
Magabatan kasar Somaliya sun sanar da hallaka mayakan Ashabab da dama a tsakiyar kasar
Akalla mayakan 'yan Ashabab 26 ne suka hallaka sannan wasu da dama na daban suka ji rauni sanadiyar wani gumurzu tsakanin su da Dakarun sa kai jihar Galmudug dake tsakiyar kasar, sanarwar ta tabbatar da cewa wasu daga cikin Dakarun yankin sun jikkata.
Usman Isa Noor jami'i mai kula da tsaron jihar Galmudug a jiya Litinin ya tabbatar da cewa Kokarin da mayakan Ashabab suka yi na sace wasu fararen hula bai ci nasara ba, sannan kuma ya bukaci Gwamnatin Somaliya da Dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar Tarayyar Afirka da su taimakawa Dakarun sa kai na yankin ta yadda za su ci gaba da kalubalantar mayakan Ashabab.
Wannan dai shi ne karo na biyu cikin maku guda da mayakan Ashabab din ke kai farmaki a yankin na Galmudug ba tare da cin nasara ba inda suke fuskantar tirjiya daga Dakarun sa kai na yankin.
Ya zuwa yanzu dai babu wani martani da kungiyar ta Ashabab ta mayar dangane da irin nasarorin da Dakarun tsaron Somaliya ke samu a kan su.