Karuwar Rashin Tsaro A Kasar Sudan Ta Kudu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i14599-karuwar_rashin_tsaro_a_kasar_sudan_ta_kudu
Yanayin Rashin Tsaro Yana Karuwa A Sudan Ta Kudu
(last modified 2018-08-22T11:29:19+00:00 )
Nov 30, 2016 06:20 UTC
  • Karuwar Rashin Tsaro A Kasar Sudan Ta Kudu

Yanayin Rashin Tsaro Yana Karuwa A Sudan Ta Kudu

A cikin makwannin bayan nan, dai sojojin da su ke biyayya ga dan tawaye, Reikh Machar, sun kai harin ba zata a garin Pay inda su ka kashe mutane 50 da kuma jikkata wasu da dama.

Hari na karshe da 'yan tawayen su ka kai, shi ne wanda su ka kashe fararen hula 21 da kuma jikkata wasu 20.

Ofishin da ke wakiltrar majalisar dinkin duniya a kasar ta Sudan ta kudu, ya yi kira da a kawo karshen tashe-tashen hankula da dawo da zaman lafiya.

Bayan jawabin karshe da Reikh Machar ya yi na ci gaba da kalubalantar gwamnatin kasar, rashin lafiya ya sake dawowa kasar.