Ganawar Ministan harakokin wajen Masar da Mataimakin Trump
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i14665-ganawar_ministan_harakokin_wajen_masar_da_mataimakin_trump
Ministan Harakokin wajen Masar da Mataimakin sabon Kasar Amurka sun tattauna kan fadada alaka da aiki tare tsakanin kasashen biyu.
(last modified 2018-08-22T06:59:19+00:00 )
Dec 01, 2016 08:16 UTC
  • Ganawar Ministan harakokin wajen Masar da Mataimakin Trump

Ministan Harakokin wajen Masar da Mataimakin sabon Kasar Amurka sun tattauna kan fadada alaka da aiki tare tsakanin kasashen biyu.

Kamfanin dillancin labaran Isna na kasar Iran ya nakalto Ahmad Abu zaid kakakin Ma'aikatar harakokin wajen Masar na cewa Ministan harakokin wajen Kasar Samih Shukri ya gana da mataimakin sabon Shugaban kasar Amurka Mike Pence a birnin Watsinton inda ya isar da sakon Shugaban kasar ta Masar Afdulfatah Alsese.

A cewar Ahmad Abu Zaid, daga cikin sakon Shugaban kasar ta Masar a kwai bukatar zababben Shugaban kasar Amurka ya taimaka wajen magance rikicin yankin da kuma yaki da ta'addanci a Duniya.