Martanin Sudan ta kudu kan zarلkin ta da kisan kare dangi
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i14719-martanin_sudan_ta_kudu_kan_zarلkin_ta_da_kisan_kare_dangi
Shugaban Kasar Sudan ta Kudu ya yi watsi da zarkin da aka yiwa Gwamnatin sa na kisan kare dangi ga wasu kabilun kasar
(last modified 2019-08-10T14:54:46+00:00 )
Dec 02, 2016 11:21 UTC
  • Martanin Sudan ta kudu kan zarلkin ta da kisan kare dangi

Shugaban Kasar Sudan ta Kudu ya yi watsi da zarkin da aka yiwa Gwamnatin sa na kisan kare dangi ga wasu kabilun kasar

Kamfanin dillancin Labaran Reuteus ya nakalto Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Keir a yayin da yake ziyarar aiki a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu na cewa zarkin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi wa Kasar sa na cewa ana kokarin shafe wata kabilar kasar ta hanyar kisan kare dangi, zarki ne da ba shi da wani tushe.

A ranar Alkhamis din da ta gabata ce Yasmin Soca Manzon musaman na Kungiyar kare hakin bil-adama ta MDD bayan ya koma gida daga kasar Sudan ta kudun ya bayyana cewa da dama daga cikin yankunan kasar Sudan ta kudun na fuskantar kisan kare dangi na kokarin shafe wasu kabilu daga cikin kasar.

Mista Yasmin Soca ya bayyana halin da kasar Sudan ta kudun ke ciki a yanzu da yanayin kisan kare dangin da ya wakana a kasar Ruwanda a shekarar 1994, kuma ya jankalin cewa kasar na iya zama wurin kisan kare dangi, idan ba dauki mataki ba.