Sojojin Kasar Somalia Sun Kashe Yayan Kungiyar Al-Shaba Guda Biyu
Jami'an sojojin kasar Somalia tare da samun tallafin sojojin kasashen waje sun sami damar hallaka mayakan kungiyar Al-shaba biyu a jiya jumma.
Kamfanin dillancin Labaran chinhuwa na kasar China ya bayyana cewa sojojin na kasar Somalia tare da tallafin sojojin Majalisar dinkin duni ya ta AMISOM sun fafata da mayakan Al-shaba a garin Wajid na lardin Bakool kadu maso yammacin kasar inda suka kashe akalla mayakan al-shabab biyu.
Wani babban jami'in sojoan kasar ta Somalia ya fadawa Xinhuwa kan cewa an soma fadan ne tun ranar Alhamis da yamma kuma an kashe sojan kasar guda an kuma raunawa wani guda. A halin yanzu dai sojojin kasar ta Somalia tare da hadin guiwa da na majalisar din kin sazu tsakake yankin Bakool daga ikon al-sahabam