An karfafa matakan tsaro a gefen Ofishin Jakadancin Amurka dake kasar Tchadi
Dec 03, 2016 11:19 UTC
Wata Majiyar tsaro a kasar Tchadi ta sanar da karfafa matakan tsaro a gefen ofishin Jakadancin Amurka dake birnin injamena
Wannan matakin tsaro na zuwa ne bayan wani harin bindiga da wani dan bindiga ya kai ranar Laraba da ta gabata, duk kuwa da cewa Jami'an tsaron sun sanar da kame maharin, amma Gwamnatin kasar ta Tchadi ta bada umarni da a karfafa matakan tsaro a kusa da Ofishin jakadancin na Amurka.
Ganin cewa kasar ta Tchadi na fuskantar hare-haren ta'addanci na kungiyar Boko haram duk wani hari da aka kai cikin kasar ana danganta shi ne da kungiyar boko haram.
Kasar Tchadi dai na taka muhimayar rawa wajen yaki da kungiyar Boko haram a yankin tabkin Tchadi.
Tags