Kungiyar AU ta yi alawadai da Harin kungiyar Ashabab A kasar Somaliya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i1477-kungiyar_au_ta_yi_alawadai_da_harin_kungiyar_ashabab_a_kasar_somaliya
Kungiyar Tarayyar Afirka ta yi alawadai da harin ta'addancin da kungiyar Ashabab ta kai garin Baidoa dake kudancin kasar Somaliya
(last modified 2018-08-22T06:57:53+00:00 )
Feb 29, 2016 12:30 UTC
  • Kungiyar AU ta yi alawadai da Harin kungiyar Ashabab A kasar Somaliya

Kungiyar Tarayyar Afirka ta yi alawadai da harin ta'addancin da kungiyar Ashabab ta kai garin Baidoa dake kudancin kasar Somaliya

Kamfanin dillancin Labaran Xin huwa na kasar China ya nakalto Fransisco Katanou manzon musaman na kungiyar Tarayyar Afirka a kasar Somaliya na cewa harin da kungiyar Ashabab ta kai garin Baidoa a daren jiya lahadi ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula da dama, kuma wanda abin bakin ciki ne domin haka kungiyar AU na yin alawadai da wannan hari na ta'addanci.

Mista Katanou ya tabbatar da cewa Dakarun Tsaron na kungiyar tarayyar Afirka tare da hadin gwiwar Dakarun tsaron kasar Somaliya da ma na wasu kasashe za su yi iya kokarinsu na ganin sun kawo karshen wannan kungiya.

A daren jiya Lahadi ne mayakan kungiyar Ashabab suka kai harin ta'addanci a garin Baidoa dake kudancin kasar inda suka kashe fararen hula kimanin 30 tare da jikkata wasu 42 na daban.

Duk da irin Dakarun tsaron da kungiyoyin kasa da kasa suka jibke a kasar Somaliya, har yanzu kungiyar Ashabab na rike a wasu yankunan kasar, lamarin da ya zamanto babbar barazana kan harakokin tsaro ga kasar da kasashen dake makonbtaka da ita.