Ci gaba da haramta buga jaridu a Sudan
Ma'aikatar leken Asirin kasar Sudan ta dakatar da wata jarida mai zaman kanta mai suna Aljarida da kuma Jaridar Almaidan mai alaka da masu Akidar gurguzu ba tare da bayyana wani dalili ba
A cikin maku guda kacal Jaridu 19 ne aka dakatar da ayiukan su a kasar ta sudan,Jami'an tsaron kasar sun bayyana cewa jaridun da aka dakatar ba sa la'akari da tsaron kasa, suna buga labarin da zai furgita jama'a su yiwa Gwamnati tawaye domin haka ne ma Ma'aikatar Leken asirin kasar ta dauki wannan mataki a kan su.
Rahoton ya ce fice gona da iri da Jaridun kasar Sudan din ke yi dangane da tsaron kasar, na kokarin tayar hankali zuwa yiwa Gwamnati bori kuma hakan ya sanya sun fuskanci dakatarwa na dan wani lokaci daga Gwamnatin kasar.
Daga cikin manyan jaridun da aka dakatar a kwai Aljarida, Al-Ayyam-Alyaumuttali, da kuma Alwatan.