'Yan tawaye sun kashe Sojojin Sudan ta kudu.
Wani sabon rikici ya barke tsakanin Sojojin Gwamnatin Sudan ta kudu da 'yan tawaye a garin Yi da yayi sanadiyar mutuwar Sojoji da dama.
Kimanin Sojoji 16 suka hallaka a wanmi sabon rikici da ya barke tsakanin Sojojin Gwamnatin Sudan ta kudu da 'yan tawaye masu biyayya da tsohon mataimakin Shugaban kasar Riek Machar a garin Yi ,Rahoton ya ce 'yan tawayen sun rusa gine gine Gwamnati a garin na Yi sannan kuma sun kwashi ganima na bindigogi da harsashe a yayin kai wannan hari.
A cikin makunin baya-bayan nan Dakarun 'yan tawaye masu biyayya da Riek Machar sun yi ta kai harin ba zata kan Dakarun Gwamnatin a kan hanyoyin dake isa zuwa garin Yi, lamarin da yayi sanadiyar hallakar Sojojin Gwamnatin da dama.
Tun bayan da madugun 'yan tawayen Riek Machar ya shelanta yaki da Gwamnatin Sudan ta kudun, Dakarun 'yan tawaye masu biyayya da shi suka kara kaimi wajen kai hare-hare kan Dakarun Gwamnatin.