Taron Matasan Kasashen Musulmi A Cibiyar Azahar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i15001-taron_matasan_kasashen_musulmi_a_cibiyar_azahar
An fara gudanar da zaman taro na matasan kasashen musulmi a babban dakin taron cibiyar jami'ar Azahar da ke birnin Alkahira na Masar.
(last modified 2018-08-22T06:59:22+00:00 )
Dec 08, 2016 14:07 UTC
  • Taron Matasan Kasashen Musulmi A Cibiyar Azahar

An fara gudanar da zaman taro na matasan kasashen musulmi a babban dakin taron cibiyar jami'ar Azahar da ke birnin Alkahira na Masar.

Kamfanin dillanicn labaran Rasa ya bayar da rahoton cewa, Abbas Shauman mataimakin babban malamin cibiyar Azhar ya bayyana  agaban taron cewa, babban aikin da ke gaban malaman addinin muslunci shi ne fadakar da matasa tare da saita tunaninsu, domin rashin yin hakan ne ke sanya matasa bin duk wani abin da ya shigo, da hakan ya hada akidun da ke kai su ga ta'addanci.

Azhar ta shirya wannan taro ne da nufin wayar da kan matasa kan sahihiyar fahimta ta addini, wadda ta ginu a kan aman lafiya da fahimtar juna a tsakanin musulmi da ma wadanda ba musulmi, da kuma isar da sakon muslunci ta hanyar kyawawan dabiu a kisa ko ayyukan ta'addanci ba.