An fara tattaunawar Siyasa a birnin Kinshasa na kasar Kwango
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i15019-an_fara_tattaunawar_siyasa_a_birnin_kinshasa_na_kasar_kwango
An fara wata sabuwar tattaunawa da nufin neman mafuta ga rikicin siyasar Kwango a birnin Kinshasa
(last modified 2018-08-22T06:59:22+00:00 )
Dec 08, 2016 14:44 UTC
  • An fara tattaunawar Siyasa a birnin Kinshasa na kasar Kwango

An fara wata sabuwar tattaunawa da nufin neman mafuta ga rikicin siyasar Kwango a birnin Kinshasa

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya habarta cewa a wannan Alkhamis babbar cocin katolikar Kwango ta bude taron tattaunawa na 'yan siyasar kasar da nufin samar da mafuta dangane da rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa tsakanin su yayin da ya rage kasa da kwanaki 15 na kawo karshen milkin Shugaban kasar Joseph Kabila.

Marcel Autamby daga cikin mahalartar taron ya shaida wa manema labarai cewa taron na yau ya hada dukkanin 'yan siyasa da dattijan kasar domin tattaunawa na neman mafutar kan rikicin siyasar da kasar ke fuskanta tare kuma da cimma matsaya kan lokacin da ya kamata a gudanar da zabe.

Gwamnatin kasar Ta kwango ta bukaci da a dage lokacin gudanar da zaben Shugaban kasar saboda dalilai na rashin kudu da kuma kayan aiki zuwa shekaru biyu masu zuwa,bukatar da 'yan adawa suka yi watsi da ita, inda su ka ce Shugaba Kabila ya dauki wannan mataki ne da nufin ci gaba da dawwama a kan karagar milki.