An karfafa matakan tsaro a kan iyakar Sudan da Libiya
Kakakin Dakarun tsaron Sudan ya sanar da karfafa matakan tsaron a kan iyakar kasar sa da kasar Libiya domin hana 'yan ta'addar IS shiga cikin kasar
Kafar watsa labaran Alyaumu sabi'i ta kasar Masar ta nakalto Ahmad Khalifa Ashami kakakin Rundunar tsaron Sudan a wannan Alkhamis na cewa Jiragen yakin kasar na sintiri a kan iyakar kasar da Libiya sannan kuma an jibke sojoji masu yawa a kan iyakar domin dakile duk kokari da mayakan IS ko kuma gungu dake dauke da makamai shiga cikin kasar daga kasar Libiya
Ashami ya kara da cewa a kwai babban sansanin Soja da aka samar a kan iyaka daga bangaren arewa maso yammacin kasar domin kai agaji a duk lokacin da wata bataliyar iyakar kasar ta bukaci hakan ,kuma ana masayar bayyanai tsakanin Rundunar Sojin saman kasar da na kasa.
Har ila yau Ashami ya yi ishara kan Dakarun hadin gwina na kasar da kasar Tchadi a kan yankunan dake kan iyakokin kasar wadanda suke sunturi domin kalubalantar masu fasa kwabri na Mutane da kwayoyi gami da haramceccen kasuwanci a kan iyakokin kasar, sannan ya ce matakin da kasashen biyun suka dauka ya rage wannan musiba.
Ana sa ran Sudan ita ce kasa ta farko da 'yan ta'addar IS ke iya gudu ciki, bayan kashin da suka sha a hanun Dakarun Libiya a birnin Sirte,a ranar Talatar da ta gabata ce Dakarun kasar Libiya suka fatattaki mayakan ISIS a tunkar su ta karshe na garin Sirte da hakan ya basu nasarar tsarkake garin daga mamayar 'yan ta'addar na ISIS.