Jami'an Tsaron Masar Sun Kama Dan Hambararren Shugaba Kasar Muhd Morsi
(last modified Fri, 09 Dec 2016 06:37:23 GMT )
Dec 09, 2016 06:37 UTC
  • Jami'an Tsaron Masar Sun Kama Dan Hambararren Shugaba Kasar Muhd Morsi

Jami'an tsaron kasar Masar sun kama dan hambararren shugaban kasar Muhammad Morsi, wato Usama Morsi saboda zargin da suke masa na kokarin tada fitina a kasar.

Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya jiyo wani babban jami'in tsaron kasar ta Masar yana cewa a jiya Alhamis ne jami'an tsaron suka yi awun gaba da Usama Morsi, wanda daya ne daga cikin 'ya'yan hambararren shugaba Morsin su biyar, a gidansa da ke yankin Delta Nil saboda zargin kokarin da yake yi na tayar da fitina a kasar.

Jami'an tsaron dai sun ce Usama Morsin yana ta kokari wajen janyo hankalin mutane da kuma tunzaru su wajen yin fito na fito da hukuma lamarin da ke barazana ga tsaro da zaman lafiyar kasar.

Tun dai bayan da sojojin kasar ta Masar suka hambarar da gwamnatin Morsin a shekara ta 2014, shekara guda bayan darewarsa karagar mulki, mahukuntan kasar Masar din suke ci gaba da dirar mikiya kan magoya bayansa da 'yan kungiyarsu ta Ikhwan saboda abin da suka kira kokarinsu da haifar da fitina sakamakon kubucewar mulki daga hannunsu.