Shugaban 'Yan Adawar Ghana Ya Lashe Zaben Shugabancin Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i15082-shugaban_'yan_adawar_ghana_ya_lashe_zaben_shugabancin_kasar
Shugaban jam'iyyar adawa ta "New Patriotic Party" a kasar Ghana Nana Akufo-Addo ya lashe zaben shugabancin kasar bayan da ya samu rinjaye a kan shugaban kasar mai ci John Dramani Mohamad.
(last modified 2018-11-18T05:33:40+00:00 )
Dec 10, 2016 02:24 UTC
  • Shugaban 'Yan Adawar Ghana Ya Lashe Zaben Shugabancin Kasar

Shugaban jam'iyyar adawa ta "New Patriotic Party" a kasar Ghana Nana Akufo-Addo ya lashe zaben shugabancin kasar bayan da ya samu rinjaye a kan shugaban kasar mai ci John Dramani Mohamad.

Hukumar zaben kasar Ghana ta sanar da shugaban jam'iyyar adawa ta "New Patriotic Party" Nana Akufo-Addo a matsayin dan takarar da ya lashe zaben shugabancin kasar da aka gudanar a ranar Laraba 7 ga wannan wata na Disamba, inda ya samu kashi 54 cikin dari na kuri'un da aka kada.

Nana Akufo-Addo dan shekaru 72 a duniya ya tsaya takarar shugabancin kasar Ghana a zabukan shekara ta 2008 da kuma 2012, inda ya sha kaye, amma a wannan karo ya samu rinjaye, inda a karkashin kundin tsarin mulkin kasar ta Ghana za a rantsar da shi a matsayin shugaban kasa a ranar 7 ga watan Janairun shekara ta 2017 mai kamawa.

Mutane kimanin 400 ne daga sassa daban daban na duniya suka halacci zaben kasar ta Ghana a matsayin masu sanya-ido a zabukan, kuma an gudanar da zabukan cikin kwanciyar hankali.