Gasar Hawa Kan Kujerar Shugabancin Tarayyar Afirka
Gasa A tsakanin Shugabancin Tarayyar Afirka
Kasashe biyar da su ke neman kujeran shugabancin cibiyar tarayyar Afirka,sun gudanar da taro domin tattaunawa.
A jiya juma'a ne dai aka yi taron a tsakanin wakilan kasashen Kenya da Gunea Conakry da Chadi da Senegal da Botswasa a birnin Adis ababa inda kowane daga cikinsu ya gabatar da mahangarsa akan manufofin nahiyar Afirka da kuma yadda za a warware takaddamar da ake yi.
Mahangar kasashen dai ta kunshi manufofin da nahiyar za ta sanya a gaba daga nan zuwa 2063, da su ka kunshi hanyoyin saukake kasuwanci da warware matsalolin cikin gida na siyasa da tsaro.
A ranakun 30 da 31 ga watan janairu ne za a yi zaben, sabon shugaban hukumar cibiyar tarayyar ta Afirka.