Zababben Shugaban Gambia Na Bin Hanyoyin Karbar Mulki Ta Ruwan Sanyi
(last modified Sat, 10 Dec 2016 18:59:41 GMT )
Dec 10, 2016 18:59 UTC
  • Zababben Shugaban Gambia Na Bin Hanyoyin Karbar Mulki Ta Ruwan Sanyi

Zababben shugaban kasar Gambia Adama Barrow ya ce yana bin dukkanin hanyoyi domin ya karbi mulki ta hanyar ruwan sanyi, tare da gamsar da Yahya Jammeh kan ya amince da kayin da ya sha kamar yadda amince da hakan daga farko.

Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya bayar da rahoton cewa, Adama Barrow ya fadi a yau cewa, yana bin dukkanin hanyoyin da suka kamata, domin samun damar gamsar da Yahya Jammeh kan ya mika mulki a wa'adin da dokar kasar ta kayyade.

A jiya ne dai Yahya Jammeh ya sanar da cewa bai amince da sakamakon zaben shugaban kasar ba, duk kuwa da cewa da farko ya amince da hakan, inda ya sha kayi a hannun babban dan takarar adawa Adama Barrow, tare da amincewa da kayin da ya sha.

Majalisar dinkin duniya da kungiyar tarayyar Afirka suna matsa lamba kan Yahya Jammeh da ya mutunta kaidoji da dokokin kasar kasar, domin kauce wa fadawar kasar cikin wani mawuyacin hali.