An Tsaurara Matakan Tsaro A Babban Birnin Kasar Gambiya
(last modified Sun, 11 Dec 2016 11:19:35 GMT )
Dec 11, 2016 11:19 UTC
  • An Tsaurara Matakan Tsaro A Babban Birnin Kasar Gambiya

Rahotanni daga kasar Gambiya sun bayyana cewar an ba za jami'an tsaro a kusan dukkanin lungunan birnin Banjul, babban birnin kasar don tabbatar da tsaro bayan da shugaban kasar Yahya Jammeh yayi watsi da sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar inda ya sha kaye.

A ranar Juma'ar da ta gabata ce dai shugaba Jammeh, cikin wani jawabi da yayi ta gidan talabijin din kasar yayi watsi da sakamakon zaben bayan da a baya ya sanar da cewa  ya amince da shi lamarin da ya sake sanya kasar cikin yanayi na dardari.

Kungiyoyin kasa da kasa dai sun kirayi shugaba Jammeh da ya girmama sakamakon da hukumar zaben kasar ta sanar ya mika mulki kamar yadda yayi alkawarin yi.

Da dama dai suna ganin matukar dai shugaba Jammeh ya ki amincewa da sakamakon da kuma tsayawa kyam sai an sake to kasar tana iya fadawa cikin wani yanayi na rashin tabbas na siyasa.