Shugaba Buhari Ya Bayyana Goyon Bayansa Kan Samar Da Kasar Palasdinu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i1516-shugaba_buhari_ya_bayyana_goyon_bayansa_kan_samar_da_kasar_palasdinu
Shugaban tarayyar Nigeria Mohammadu Buhari ya bayyana cikekken goyon bayansa ga samar da kasashen Palasdinu
(last modified 2018-08-22T06:57:53+00:00 )
Mar 01, 2016 08:31 UTC
  • Shugaba Buhari Ya Bayyana Goyon Bayansa Kan Samar Da Kasar Palasdinu

Shugaban tarayyar Nigeria Mohammadu Buhari ya bayyana cikekken goyon bayansa ga samar da kasashen Palasdinu

Shugaban tarayyar Nigeria Mohammadu Buhari ya bayyana cikekken goyon bayansa ga samarda kasashen Palasdinu - Israela don kawo karshen rikicin gabas ta tsakiya. Shugaban ya bayyana haka ne a lokacinda yake ganawa da sarkin Qatar Tamim Bin Hammad Al-thani a ranar lahadin da ta gabata.

Kakakn fadar shugaban kasa Mr Femi Adisana ne ya bayyana haka a jiya ya kuma kara da cewa shugaba Buhari ya ce gwamnatin Nigeria zata tsaya kai da fata don ganin an samar da kasar Palasdinu wacce take da birnin Qudus a matsayin babban birni. Buhari ya kara da cewa gwamnatinsa tana goyon bayan dukkan kudurorin da komitin tsaron majalisar dinkin duniya ta samar don samar da zaman lafiya a duniya. Dangane da kasar Palasdinu ma Nigeria tana goyon bayan kasar Palasdinu mai kan iyakoki na shekara 1967.

Dangane da faduwar farashin man fetur daga $100 zuwa $ 30 kuma shugaban ya ce wannan halin bai kamata ya ci gaba ba.