Shugaban Kasar Sudan Ya Yi Barazanar Murkushe Masu Adawa Da Gwamnatinsa
shugaban kasar Sudan Umar Hassan Albashir ya yi barazanar murkushe duk wata zanga-zangar nuna adawa da gwamnatinsa a kasar.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya habarta cewa, a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a yau a wata ziyara da ya kai a jahar Kassala, Albashir ya yi kashedin cewa, zai dauki dukkanin matakan da suka dace domin murkushe zanga-zangar da jam'iyyun adawa da kungiyoyin farar hula ke shirin gudanarwa akasar, kamar yadda aka murkushe zanga-zangar shekara ta 2013.
Jam'iyyun adawa da kungiyoyin farar hula a kasar Sudan, suna kiran magoya bayansu da su zama cikin shiri domin gudanar da wata gagarumar zanga-zanga a fadin kasar, da nufin nuna rashina mincewa da salon mulkin Alabshir wanda suka bayyana shi da kama karya, inda suka ce sun gaji da wahalhalun da mulkin Albashir ya jefa su ciki, dukkanin kayan masarufi sun yi tsada, abinci na neman ya gagari talaka a kasar.