Tawagar ECOWAS Ta Isa Gambia Don Tattaunawa Da Shugaba Yahyah Jame
Shugaban tarayyar Nigeria tare da tawagar ECOWAS sun isa kasar Gambia don shawo kan shugaba Jame ya rungumi kaddara ya mika mulki ga zabebben shugaban kasar a cikin wata mai kamawa.
Kamfanin dillanin labaran NAN na Nigeria ya bada labarin cewa shugaba muhammadu Buhari da wasu shuwagabannin yammacin Afrika sun isa birnin Banjul don ganawa da shugaba Yaha Jameh kan ya mika shugabancin kasar ga zabebben shugaban kasa a cikin watan Jeneru mai kamawa.
Labarin ya kara da cewa shugaba Buhari ya isa birnin na Banjul tare da shugaban kasar Liberia kuma shugaban kungiyar ECOWS Miss Ellen Johnson -Sirlif da kuma shugba kasar Salio Ernest Bai Koroma. Kafin isowarsu dai shugaban kasar Ghana mai barin gado John Dramani Mahama ya isa birnin na Banjul don shiga cikin tawagar ECOWAS wacce zata yi kokarin gamsar da shugaban na kasar Gambia ya sauka daga kujerar shugabancin kasar, ya kuma mutunta kundin tsarin mulkin kasar.
Shugaba Jameh dai ya fadi a zaben shugaban kasa da aka gudanar a kasar a cikin kwanakin da suka gabata, har ma ya taya abokin hamayyarsa a zaben Adama Barrow wanda ya lashe zaben murna da zabensa amma bayan yan kwanaki sai kuma ya lashe amansa inda ya ki amincewa da sakamakon zaben kuma.
A halin yanzu dai jam'iyyar shugaba Jameh ta bada sanarwan cewa zata shigar da kara a wata babban kotun kasar don ganin nan rasu sakamakon zaben a kuma zake wani sabon zaben.