ISIS Ta Dauki Alhakin Harin Ta'addancin Birnin Alkahira
Kungiyar 'yan ta'addan takfiriyyah ta ISIS (Daesh) ta sanar da cewa ita ce ke da alhakin kaddamar da hari kan cocin Kibdawa a birnin Alkahira na kasar Masar.
Kungiyar ta sanar da hakan ne a shafinta na yanar gizo, inda ta bayyana hakan a matsayin wani babban aikin jihadi.
Kafin wannan lokacin dai mahukuntan Masar sun zargi jagororin kungiyar 'yan musulmi da ke zaune a kasar Qatar da hannua a cikin lamarin, kasantuwar wanda ya kai harin yana zaune a kasar Qatar tun kimanin shekaru biyu da suka gabata.
Mutane 27 ne suka rasa rayukansu sakamon kai harin, yayin da wasu fiye da 50 suka samu munan raunuka.
Shugaban kasar ta Masar Abdulfattah Sisi ya sanar makoki na tsawon kwanki uku a fadin kasar, domin nuna alhini kan abin da ya faru.