Tawagar ECOWAS Ta Kasa Cimma Matsaya Tare Da Yahya Jammeh Na Gambia
(last modified Wed, 14 Dec 2016 10:02:03 GMT )
Dec 14, 2016 10:02 UTC
  • Tawagar ECOWAS Ta Kasa Cimma Matsaya Tare Da Yahya Jammeh Na Gambia

Shugabar kasar Liberia Ellen Johnson Sirleaf, wadda ta jagoranci tawagar kungiyar ECOWAS zuwa kasar Gambia a jiya Talata wadda ta hada har da shugabannin Najeriya da Ghana, ta bayyana cewa ba su cimma wata matsaya tare da Yahya Jammeh kan warwaren rikicin siyasar kasar ba.

Ellen Johnson Sirleaf ta bayyana cewa sun bukaci Yahya Jammeh da ya mutunta sakamakon zaben shugaban kasar, ya kuma karbi kayen da yasha kamar yadda ya yarda da hakan tun daga farko, amma ga dukkanin alamu bai gamsu da hakan ba.

Tun kafin wannan lokacin dai jam'iyyar Yahya Jammeh mai mulki  akasar ta bukaci babbar kotun kolin kasar da ta soke sakamakon zaben, kamar yadda a jiya sojoji suka mamaye babban ginin hukumar zaben.

Majalisar dinkin duniya gami da kungiyar tarayyar Afirka sun yi tir da Allawadai da matakin da Jammeh ya dauka na kin amincewa da sakamakon zaben shugaban kasar da aka gunar a kasar ta Gambia, tare da bayyana hakan a matsayin lamari mai matukar hadari ga makomar kasar.