An kori ma'aikatan Agaji biyu a kasar Sudan ta Kudu
Gwamnatin Sudan ta kudu ta kori wasu jami'an kai agajin gaggauwa biyu daga cikin kasar
Rahotanni dake fitowa daga birnin Juba na kasar Sudan ta kudu sun habarta cewa a cikin Makun da ya gabata, Gwamnatin kasar ta bukaci wasu magabatan kungiyar kai agaji ta NRC biyu da su fice daga cikin kasar ba tare da bayyana wani dalili ba.
A nata bangare kungiyar ta NRC ta tabbatar da wannan labari, inda ta ce a ranaikun Juma'a da Talatar da suka gabata ce Gwamnatin Sudan ta Kudu ta bukaci wasu manyan jami'anta biyu dake aikin agaji a cikin kasar da su fice daga cikin kasar.
Tun daga shekarar 2014 ne kungiyar Agajin ta NRC ke gudanar da aiyukan Agaji a kasar Sudan ta kudun, a cikin watani takwas na farko kungiyar ta taimakawa Mutane sama da dubu 658 a kasar.
Wannan mataki dai na zuwa ne bayan da magabatan Sudan ta kudun suka kori wani Dan Jarida na kasar Amurka, sannan kuma suke ci gaba da fuskantar matsin lamba daga kungiyoyin kare hakin bil-adama na Duniya, inda suke ci gaba da bayyana fargabarsu dangane da kisan kare dangi da Gwamnatin Sudan ta kudun ke yiwa wasu kabilun kasar.