Kungiyar AU Ta Nuna Damuwa Kan Yiyuwar Shigowar 'Yan Ta'adda Nahiyar Afirka
Kwamitin sulhu da tsaro na kungiyar Tarayyar Afirka ya bayyana tsananin damuwarsa dangane da yiyuwar dawowar dubun dubatan 'yan ta'adda nahiyar Afirka bayan shan kashin da suke fuskanta a Siriya da Iraki.
Kamfanin dillancin labaran Iran IRNA ya jiyo babban kwamishinan kwamitin sulhu da zaman lafiya na kungiyar Tarayyar Afirkan Isma'il Sharqi, a jawabin da ya yi wajen taron tattaunawa kan ayyukan ta'addanci da ake gudanarwa a kasar Aljeriya yana fadin cewa bisa bayanan da suka samu, 'yan ta'addan da suke shan kashi a Siriya da Iraki suna shirin gudu daga wadancan kasashen zuwa kasar Somaliya.
Har ila yau kuma yayin da yake nuna damuwarsa dangane da kokarin da wadannan 'yan ta'addan suke yi na komawa kasashen da suka fito na daga Turai da Afirka bayan shan kashin da suke fuskanta a kasashen Siriya, Iraki Da Yemen, Mr. Sharqi ya ce kasashen da suke makwabtaka da Tekun Chadi da yankunan Sahel suna fuskantar babbar barazana ta tsaro, don haka akwai bukatar aiki tare tsakanin kasashen nahiyar Afirka don magance wannan barazanar.
Rahotanni dai suna nuni da cewa 'yan ta'addan da aka shigo da su kasashen Siriya da Iraki Da Yemen, a halin yanzu suna cikin tsaka mai wuya sakamakon kashin da suke ci gaba da sha a wajen dakarun gwamnatin wadannan kasashen lamarin da ke tilasta musu tunanin komawa kasashen da suka fito.