Ana gudanar da Zaben 'yan majalisar dokoki a Cote d'Ivoir
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i15436-ana_gudanar_da_zaben_'yan_majalisar_dokoki_a_cote_d'ivoir
A wannan Lahadin ne Al'ummar kasar Cote d'Ivoir fiye da miliyan shida ke zaben 'yan majalisun dokokin kasar 255.
(last modified 2018-08-22T06:59:24+00:00 )
Dec 18, 2016 12:02 UTC
  • Ana gudanar da Zaben 'yan majalisar dokoki a Cote d'Ivoir

A wannan Lahadin ne Al'ummar kasar Cote d'Ivoir fiye da miliyan shida ke zaben 'yan majalisun dokokin kasar 255.

Wannan zabe na a matsayin na farko a karkashin sabuwar jamhuriya ta uku bayan zaben rabagardama da ya amince da sabon kundin tsarin mulkin kasar a watan Oktoban da ya gabata. Da misalin karfe takwas ne dai agogon GMT aka buda runfunan zabe kimanin 19,800 a fadin kasar gaba daya.

A cewar Shugaban hukumar zaben kasar CEI, Yousouf Bakayoko za a rufe runfunan zaben ne da misalin karfe shida na yamma agogon GMT, sannan kuma sakamakon zaben zai iya kai wa ranar Laraba kafin a same shi, sai dai kuma ana iya samun sakamakon wuccin gadi kafin wannan rana.

Duk da ana cewa mata za su taka rawar gani a fagen siyasar kasar ta Cote d'Ivoir, amma kungiyar mata da ke fafutikar samun daidaito tsakanin maza da mata a kasar, na ganin cewa babu takarar mata da yawa a zaben, inda ta ce mata 43 ne kawai daga cikin 'yan takara 1,337 ke yin takarar.