An kashe Mutane 7 a Jumhoriyar Demokaradiyar Kwango
A yayin da kasar Kwango ke funkanta rikicin Siyasa, an kashe Mutane 7 a gabashin kasar
Kamfanin dillancin labaran Faransa ya habarta cewa a jiya Litinin 'yan tawayen Mai Mai na kasar Kwango sun kai hari a wani gidan Kaso na garin Butembo dake gabashin kasar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar 'yan tawaye biyar, jami'in wanzar na zaman Lafiya dan kasar Afirka ta kudu guda da kuma jami'in 'yan sanda guda. a cikin 'yan watanin nan 'dai yan tawayen Mai Mai sun yi ta kai hare hare a garin na Butembo.
A bangare guda taho mu gama tsakanin Jami'an 'yan sanda da 'yan awada na ci gaba da rura rikicin siyasar kasar, dage zaben shugaban kasar da Gwamnati ta yi a watan da ya gabata yayi sanadiyar zanga-zangar nuna adawa da wannan mataki a birnin Kinshasa fadar milkin kasar da kuma sauran manyan buranan kasar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwa da kuma jikkatar mutane da dama
A ranar 11 ga watan Nuwambar da ya gabata ne, Kotun kare kundin tsarin milkin kasar ta Kwango ta bayar da hukunci cewa matukar dai ba a gudanar da zaben Shugaban kasar ba zuwa karshen wa'adin Shugaba Joseph Kabila da ya kare a daren jiya Litinin, Shugaban na iya ci gaba da gudanar da milki har lokacin da ake gudanar da zabe a kasar, hukuncin da 'yan adawa suka yi watsi da shi.