An Kafa Kwamitin Binciken Sakamakon Zaben Shugaban Kasar Zambia
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i15538-an_kafa_kwamitin_binciken_sakamakon_zaben_shugaban_kasar_zambia
Shugaban kasar Zambia Edgar Lungu ya sanar da kafa wani kwamitin gudanar da bincike kan zaben shugaban kasar d akuma na kanan hukumomi.
(last modified 2018-08-22T06:59:25+00:00 )
Dec 21, 2016 13:07 UTC
  • An Kafa Kwamitin Binciken Sakamakon Zaben Shugaban Kasar Zambia

Shugaban kasar Zambia Edgar Lungu ya sanar da kafa wani kwamitin gudanar da bincike kan zaben shugaban kasar d akuma na kanan hukumomi.

Majiyoyin fadar shugaban kasar ta Zambia sun sanar da cewa, shugaba Edgar Lungu ya kafa kwamitin ne daidai da dokokin kasar, wanda ya kunshi mambobi 15 da suka hada har da alkalin alkalai na kasar, kuma a shirye yake ya amince da dukkanin abin da kwamitin ya gabatar masa.

Jam'iyyun adawa a kasar zambia dai sun nuna korafinsu dangane da sakamakon zaben shugaban kasar da na kananan hukumomi da aka gudanar a cikin watan Agustan da ya gabata, inda suke zargin an tafka magudi wanda ya baiwa jam'iyyar shugaban kasar nasara.