Cocin Katolika Ya Kirayi 'Yan Siyasan Kongo Su Kawo Karshen Rikicin Kasar
A yayin da rikicin siyasa ke ci gaba da muni a kasar Demokradiyyar Kongo, Cocin Roman Katolika, wanda ke shiga tsakani a rikicin ya kirayi shugabannin siyasar kasar da su cimma wata yarjejeniyar ta kawo karshen rikicin da ya kunno kai kafin ranar Kirsimeti.
Shugaban kungiyar CENCO din mai shiga tsakanin Mansignor Marcel Utembi ne ya bayyana hakan ne inda ya ce fatan da suke da shi ne a kawo karshen rikicin kafin ranar Kirsimetin don kawo karshen zubar da jinin da ake yi.
Wannan kira da fada-fadan cocin da suke shiga tsakanin gwamnati da 'yan adawa a rikicin ya zo bayan da rikici ya barke a kasar ta Demokradiyyar Kongon sakamakon kin sauka daga karagar mulki da shugaban kasar Joseph Kabila wanda wa'adin mulkinsa ya kare a ranar 19 ga watan Disamban nan yayi, lamarin da 'yan adawan suka ce ba za su taba amincewa da shi ba.
Rahotanni dai sun ce ya zuwa yanzu sama da mutane 20 ne suka rasa rayukansu sakamakon wannan rikici da ya barke kana wasu kuma sama da 50 suka sami raunuka.