Za'a Saki Tsohon Gwamnan Jihar Delta Daga Kurkuku A Kasar Britania
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i15580-za'a_saki_tsohon_gwamnan_jihar_delta_daga_kurkuku_a_kasar_britania
James Ibori tsohon gwamna jihar Delta a yankin niger deltar na nigeria ya sami 'yencinsa bayan dauri na akalla shekaru 7 a wani gidan yari a kasar Britania saboda zamba da al-mundahana.
(last modified 2018-08-22T06:59:25+00:00 )
Dec 22, 2016 07:47 UTC
  • Za'a  Saki Tsohon Gwamnan Jihar Delta Daga Kurkuku A Kasar Britania

James Ibori tsohon gwamna jihar Delta a yankin niger deltar na nigeria ya sami 'yencinsa bayan dauri na akalla shekaru 7 a wani gidan yari a kasar Britania saboda zamba da al-mundahana.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewa James Ibori ya taba zama gwamna a jihar Delta tsakanin shekara 1999-2007, kuma yana zaman kaso a kasar Britania tun shekara ta 2012 bayan ya amince da tuhume tuhume goma da aka yi masa wadanda suka hada da zamba da almundaha da kudade.

A halin yanzu dai James Ibori ya shafe rabin hukuncin da aka yanke masa na shekara 13, sai dai wata majiya ta bayyana cewa sakataren harkokin cikin gidan Britania ya bukaci kotu ta yi masa  daurin talala har sai ya biya wasu kudade dalar Amurka million 22 a maimakon sakinsa baki daya, sai dai alkalin kotun bai amince da hakan ba. 

A halin yanzu dai Ibori yana daga cikin hamshakai masu kudi a tarayyar Nigeria.