Kungiyar EAC Ta Karbi Sudan Ta Kudu A Matsayin Mamba
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i1570-kungiyar_eac_ta_karbi_sudan_ta_kudu_a_matsayin_mamba
Kungiyar kasashen da ke yankin gabashin Afrika EAC ta karbi sabuwar kasar Sudan ta kudu a matsayin mamba a kungiyar da ke bunkasa dangantaka da kuma kasuwanci tsakanin mambobin ta.
(last modified 2018-08-22T06:57:53+00:00 )
Mar 02, 2016 14:41 UTC
  • Kungiyar EAC Ta Karbi Sudan Ta Kudu A Matsayin Mamba

Kungiyar kasashen da ke yankin gabashin Afrika EAC ta karbi sabuwar kasar Sudan ta kudu a matsayin mamba a kungiyar da ke bunkasa dangantaka da kuma kasuwanci tsakanin mambobin ta.

Shugaban kungiyar kuma shugaban kasar Tanzania ne John Magufuli ya sanar da haka a wannan Larabar yayin wani taron a birnin Arusha dake arewa maso gabashin kasar Tamzaniya.

kungiyar da ke da cibiya a birnin Arusha na kasar Tanzania yanzu dai ta kunshi mambobi shida da suka hada da Burundi da Kenya da Rwanda da Tanzania da Uganda, wanda a jimilce suka da yawan al'ummar data kai sama da miliyan 150.

Sudan ta Kudu wadda ta sami 'yancin kai a shekarar 2011 daga Sudan, ta fada cikin rikici ne a watan Disamba ne shekara 2013 bayan da shugaban kasar Salva Kiir ya zargi tsohon mataimakin sa Riak Machar da yunkurin kifar da mulkin sa, al’amarin da ya kai ga rasa rayukan dubban mutane tare da tilasta wa sama da miliyan 2,3 tserewa daga gidajensu, baya ga ragargaza tattalin arzikin kasar da karya darajar kudin ta, tare da haifar da koma baya a arzikin man fetur kin da Allah ya hore mata.