Kenya: Tsauraran Matakan Tsaro Saboda Tsoron Ta'addanci A Lokacin Bukukuwan Kirsimeti.
Gwamnatin Kasar Kenya ta sanar da tsaurara matakan tsaro a duk fadin kasar domin dakile duk wani yunkurin harin ta'addanci na kungiyar al-Shabab.
Gwamnatin Kasar Kenya ta sanar da tsaurara matakan tsaro a duk fadin kasar domin dakile duk wani yunkurin harin ta'addanci na kungiyar al-Shabab.
Wani jami'in gwamnatin kasar ta Kenya, Kotsuwa Olakahe ya ce, saboda harin da kungiyar ta al-shabab ta kai a cikin wasu yankuna, jami'an tsaro na 'yan sanda da jami'an ciki za su watsu a dukkanin fadin kasar domin sanya idanu akan kai da komowar 'ya'yan kungiyar ta al-shabab.
Tun da fari ministan harkokin cikin gidan kasar ta Kenya Joreph Nikaysari ya sanar da cewa; Gwamnatin kasar ta daura damarar murkushe kungiyar ta al-shabab.
Kungiyar al-shabab dai mai alaka da alqaida a kasar Somaliya ta zama babbar barazanar tsaro da kasar Kenya ta ke fuskanta. A cikin shekaru biyu na bayan nan dai kungiyar dai ta kashe daruruwan 'yan kasar Kenya.