Habasha Ta Gargadi Kasar Masar Akan Taimakawa'Yan Adawa
(last modified Tue, 27 Dec 2016 06:51:14 GMT )
Dec 27, 2016 06:51 UTC
  • Habasha Ta Gargadi Kasar Masar Akan  Taimakawa'Yan Adawa

Habasha ta ce; Masu Adawa da gwamnatin Kasar suna gudanar da ayyukansu cikin 'yanci a birnin Alkahira.

Ministan harkokin wajen kasar Habasha,, Dr.Werkineh Gebeyehu wanda ya bayyana hakan, ya kara da cewa; 'yan adawar suna gudanar da taruka cikin 'yanci da kuma watsa labarun fada da gwamnatin Habasha.

Kawo ya zuwa yanzu dai babu wani martani da ya fito daga gwamnatin Masar akan zargin da Habasha ta yi mata.

Mahukuntan Masar sun nuna rashin jin dadinsu da dasawar da ake yi tsakanin Saudiyya da Habasha, wacce ta hada da ziyarar da Ahamd khatib makusancin sarkin Saudiyya zuwa Habasha da ziyartar da ya yi wa madatsar ruwan Millenium. Haka nan kuma alkawalin da Saudiyyar ta yi na zuba hannun jari a cikin madatsar.

Gina madatsar ruwan na Millinium da Habasha ta ke yi, idan ya kammala zai rage ruwan da ya ke kwarara cikin tekun Nili.