Najeriya : An Gano Ma'aikatan Bogi 50,000
Gwamnatin Najeriya ta sanar da Gano wasu ma'aikatan bogi su 50,000 lamarin daya taimaka mata wajen ceto makudan kudade da yawansu ya kai Miliyan 630 na (Euro) kwatamcin Bilyan 13 na Niara, kamar yadda fadar shugaban kasar ta sanar.
Da yake bayyana hakan, kakakin fadar gwamnatin kasar Garba Shehu ya ce daga cikin albashin watan Fabrairu zuwa Disamba ne aka gudanar da wannan aikin wannan ya taimaka matuka wajen tattalin asusun gwammnati.
A hannu daya kuma kakakin fadar gwamnatin ya ce tuni aka gurfana da mutane 11 daga cikin wadanda suke da hannu a wannan aika-aika gaban kwamitin kasar na yaki da yiwa tattalin arzikin kasar tu'annati wato EFCC.
Mista Shehu ya kara da cewa matakin shugaban kasar na yaki da cin hanci da yiwa tattalin arzikin kasar zagon kasa domin shinfida mulki na gari na nan daram kuma ana ci gaba da aikata shi ta hanyar binciken albashin ma'aikatan gwamnati.
Shugaban na Najeriya Muhamadu wanda ke shugabancin kasar kasar tun cikin shekara 2015, yayi alkawarin yaki da cin hanci da karbar rashawa dake zamen karfen kafa ga tattalin arzikin kasar wanda gwamnatinsa ke zargin mahukuntan da suka gabata da wawushe dukuyar kasar.
A makon daya gabata dai gwamnatin Buhari tayi alkawarin bayar da kyautar kudi mai tsoka da kariya ga duk wanda ya fallasa wata haraka ta cin hanaci ko karkata kudaden al'umma a daidai wannan lokaci da tattalin arzikin kasar ke cikin tsaka mai wuya.