Mozambique : Renamo Za Ta Tsagaita Bude Wuta Na Mako Guda
Babbar jam'iyyar adawa a kasar Mozambique (Renamo) ta sanar a jiya Talata cewa, dakarunta za su tsagaita bude wuta har na tsawon mako guda.
Sanarwar ta Renamo ta zo ne kwana guda bayan babban madugunta Afonso Dhlakama ya yi wata zantawa ta wayar tarho da shugaban kasar ta Mozambique Filipe Nyusi, wanda ya kai ziyarar aiki a arewacin lardin Nampula, wanda shi ne lardi mafi yawan jama'a a kasar.
Madugun 'yan adawar ya bayyana cewa, jam'iyyar adawar ta dauki wannan mataki ne domin baiwa alummar kasar ta Mozambica damar gudanar da shagulgulan karshen shekara cikin kwanciyar hankali.
Dama dai tun a ranar Litinin, shugaba Nyusi na kasar ya yi fatar jam'iyyar adawar ta dauki wannan mataki, bayan wata tattaunawa mai armashi da ta gudana tsakanin bangarorin biyu ta wayar tarho.