Gwamnatin Tarayyar Nijeriya Ta Gano Ma'aikatan Boge Dubu 50 A Kasar
(last modified Wed, 28 Dec 2016 11:21:35 GMT )
Dec 28, 2016 11:21 UTC
  • Gwamnatin Tarayyar Nijeriya Ta Gano Ma'aikatan Boge Dubu 50 A Kasar

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta sanar da cewa ta gano ma’aikatan boge akalla dubu 50 a fadin kasar wanda hakan ya ba wa gwamnatin tarayyar damar tsimin kudaden da yawansu ya kai Naira biliyan 200 tsawon wannan shekara ta 2016 da ke karewa.

Mai magana da yawun shugaban kasar Muhammadu Buhari, wato Garba Shehu ne ya sanar da hakan inda ya ce gwamnatin Tarayyar ta sami nasarar kawar da wasu ma'aikatan boge 50,000 daga cikin jerin wadanda ake biyansu albashi lamarin da ya ba wa gwamnatin damar ajiye kudaden da suka kai Naira biliyan 200 cikin shekara mai karewar.

Malam Garba Shehu ya ci gaba da cewa tuni aka cafke  mutane 11 da suke da hannu cikin wannan almundahana da kuma yaudarar inda aka mika su ga  hukumar EFCC mai yaki da rashawa da ta'annuti ga baitul malin kasar.

Kakakin Shugaban Nijeriyan ya kara da cewa gwamnatin ta fara gudanar da wannan shirin ne a watan Fabairun da ya gabata da nufin tantance ma’aikatan gaskiya da na boge inda ya ce hakan ya ba wa gwamnatin damar tsimin Naira biliyan 13 a kowane wata a halin yanzu.