Gwamnatin Kasar Masar Ta Tabbatar Sayarwa Saudia Tsibiran Kasar Guda Biyu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i15874-gwamnatin_kasar_masar_ta_tabbatar_sayarwa_saudia_tsibiran_kasar_guda_biyu
Gwamnatin kasar Masar a jiya Alhamis ta tabbatar da sayarwa kasar Saudia tsibiran kasar guda biyu da suke a cikin Bahru Malia
(last modified 2018-08-22T06:59:27+00:00 )
Dec 30, 2016 01:10 UTC
  • Gwamnatin Kasar Masar Ta Tabbatar Sayarwa Saudia Tsibiran Kasar Guda Biyu

Gwamnatin kasar Masar a jiya Alhamis ta tabbatar da sayarwa kasar Saudia tsibiran kasar guda biyu da suke a cikin Bahru Malia

Wata tashar television na gwamnatin kasar, a jiyar Alhamis ta tabbatar da cewa gwamnarin kasar ta amince da mayarwa gwamnatin kasar Saudia tsibiran Teeron da Sanafir da suke cikin tekun red sea ga kasar Saudia, kuma tuni ta aiki da bukatar zuwa majalisar dokokin kasar don samun amincewar ta.

Labarin ya kara da cewa a farkon watan da muke ciki wata tawaga ta masu kisahin kasa suka bukaci wata kotu a birnin Alkahira ta tabbatar da hukuncin wata kotu na tabbatar da hukuncin hana saida wadan nan tsibiran ga kasar Saudia.

A cikin watan Afrilun wannan shekara ne shugaban kasar ta Masar Abdulfatah Sisi ya rattaba hannu kan wata yerjejeniya da sarkin salman bin Abdul-Azeez kan mallakarwa saudia tsibiran guda biyu. Sai dai bayan haka ne mutanen kasar sukayi na zanga zangar nuna rashin amincewar da saida wadannan Tsirinn .